<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>344</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Sai ku tashi, duk ƴan'uwa, ji kiran Nijeriya!
 Da aminci, ƙwazo, ƙauna, yi wa tasar hidima,
 Ƙoƙarin jarumai na dā ba banza ya ke ba!
 Da dukan ƙarfinku,
 Tsare salama da ƴanci, da ɗayantuwarku !

[V2]
 2) Ya Mahaliccin duniya, ka bi da manyanmu
 Har su ciccika nufinka. Taimaki duk ƴaƴanmu
 Su girma cikin gaskiya, ƙauna, da adalci.
 Ka mai da Nijeriya
 Wurin da kowa zai zauna da kwanciyar hankali!</lyrics>
<title>Sai Ku Tashi, Duk Ƴan'uwa LW344</title>
</song>